A Najeriya, ana sa ran kwamitin zartarwar babbar jam’iyyar hamayya ta PDP na kasa, zai yi zama, inda za a yi ta ƙare dangane da batun yankin da zai fitar da dan takarar shugaban kasa da kuma raba sauran mukamai da suka shafi kwamitin gudanarwar jam`iyyar a tsakanin shiyyoyin kasar.
Takaddama ta kaure a jam’iyyar bayan kwamitin raba muƙaman ya keɓe wa arewacin Najeriya kujerar shugaban jam’iyya, alamar da ke nuna cewa bangaren kudu ne zai fitar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Ibrahim Tsauri, ya shaida wa BBC cewa, zai tattauna a kan maganar rabon mukamai.
“Kwamitin zartarwa ne daman ya kafa wannan sabon kwamitin, kuma ya gama aikin shi, don haka zai dawo wa kwamitin zartarwa abin da ya samu, a duba abin da aka yi da nazari a amince ko a yi gyare-gyare ko ma ƙin amincewa da shi, daga nan sai a san abin da ake ciki,” in ji Sanata Tsauri.