Biyo baya kashin da ta sha har gida a hannu kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, a wasan mako na 29 a gasar Laligar Kasar Spaniya da ci 4-0, shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Florantina Perez yace zai yi duk mai yiyuwa wajan daukar dan wasa Kylian Mbappe Ko Earling Haaland.
A wata ganawar sa da manema labarai a birnin Madrid na Kasar ta Spaniya, Perez yace matsalar rashin kwararrun ‘yan gaba a kkungiyar ta real shine ya haifar da rashin nasarar da kungiyar tayi a wasan hamayya na El-Classico a suka kara a ranar 20 ga watan Maris na shekarar 2022, duba da cewa rashin dan wasa karim Benzema wanda shine jagoran tafiyar kungiyar ya taka rawa wajen rashin nasarar tasu.
Perez ya kara hakurkurtar da magoya bayan kungiyar kan cewa zai sa kaimi wajen daukar daya daga cikin wadannan ‘yan wasa.