Rashin karance-karancen littatafai na durkusar da al’adunmu-Sarkin Kano.

Sarkin Aminu Ado Bayero ya nuna damuwarsa kan watsi da aka yi da dabi’ar karance-karancen littatafai a fadin kasar nan.

Sarkin ya bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da wani littafi mai suna ’’Audacity of the African Child’’ da Khuraira Musa ta wallafa.

Sarkin ya ce galibi dalibai a wannan lokaci na karatu ne kawai don su ci jarrabawa, ba da zummar yin karatu ba don ya kaifafa musu tunani.

Ya ce galibi dalibai na bata lokutansu wajen bibiyar shafukan sada zumunta wanda hakan ke kara ruruta yaduwar labaran da basu da inganci. Sarki Aminu Bayero, ya ce tun daga gudummuwar marubuta irinsu Zainab Alkali, ba’a sake samun rukunin mata marubuta ba, inda yake fatan marubu ta irin su Khuraira zasu dora daga inda aka tsaya ta fuskar adabi.

Leave a Reply