Gwamnatin kasar Rasha ta shaidawa hukumar dake sa’ido kan harkokin nukiliya ta duniya cewa, a yanzu haka yankin da babbar tashar nukiliya ta kasar Ukraine take, yana karkashin ikonta.
Hukumar nukiliyar, tace kasar Rashan ta bata tabbacin cewa ma’aikatan kasar Ukraine dake aiki a tashar na cigaba da gudanar da ayyukansu.
Sai dai hukumar nukiliyar Ukraine tace tana tattaunawa da dukkanin tashoshinta na nukiliyar, kuma aiki na cigaba da gudana a dukkanninsu.
Sai dai darakta Janar na hukumar nukiliyar ta duniya, Rafael Grossi, ya shaidawa taron manema labarai cewa halin da ake ciki na da tayar da hankali