Rasha ta zargi Ukraine da yunƙurin kashe Putin

Rasha ta zargi Ukraine da yunƙurin hallaka shugabanta Vladimir Putin bayan da ta harbo wasu jirage biyu marasa matuƙa da suka riƙa shawagi a Moscow cikin daren jiya.

Bidiyon da ba a tantance ba, da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna wani abu na shawagi a sararin samaniyar fadar gwamnatin ƙasar kafin ya tarwatse.

Ukraine ta ce babu abin da zai sa ta kai hari da jirgi maras matuƙi.

Mai magana da yawun shugaban Ukraine ya ce a yanzu abin da ke gaban Ukraine shi ne ƙwato yankunanta da ke hannun dakarun Rasha.

Wani jami’i ya shaida wa BBC cewa wannan lamari alama ce da ke nuna cewa dole Rasha da shirya wa takalar faɗa daga Ukraine.

Rasha ta ce ta lalata jiragen biyu marasa matuƙa da suka yi shawagi a fadar Kremlin.

Mai magana da yawun Mista Putin ya ce shugaban ba ya fadar a lokacin da jiragen suka riƙa shawagin.

Leave a Reply