Rasha na luguden makamai masu linzami ta sama da ta ruwa zuwa Ukraine

Ana ci gaba da fitar da gargaɗin hare-hare ta sama a faɗin Ukraine a yayin da Rasha ke luguden makamai masu linzami zuwa wasu manyan biranen ƙasar.

Mai bai wa shugaban ƙasar shawara Mykhailo Podolyak ya ce fiye da makamai masu linzami 120 ne Rashar ta harba kan gine-ginen fararen hula.

Magajin garin birnin Kyiv ya ce akalla mutum uku ne ciki har da wata yarinya mai shekara 14 aka kai asibiti bayan wata fashewa a birnin

Haka kuma an ji ƙarar abubuwan fashewa a biranen Kharkiv da Odesa da Lviv da kuma birnin Zhytomyr.

Gwamnan lardin Odesa da ke kudancin ƙasar ya ce an samu ƙaruwar sabbin hare-haren makamai masu linzami a faɗin Ukraine.

Rundunar sojin saman Ukraine ta ce ƙasar Rasha na kai wa Ukraine farmaki da makamai masu linzami daga ɓangarori daban-daban ta sama da ta ruwa.

Haka kuma rahotonni sun ce rasha na amfani da jirage marasa matuƙa masu yawa domin kai hare-haren.

A yau Alhamis da safe an yi ta jin ƙararrawar gargaɗin hari ta sama a duka yankunan ƙasar.

Mai bai wa shugaban kasar shawara Oleksiy Arestovych ya umarci fararen hula a kasar da su nemi mafaka, yayin da dakarun sojin saman ke bakin ƙoƙarinsu.

Leave a Reply