Ranar Tarihi – Yau Murtala Muhammed Ya Cika Shekaru 48 Da Rasuwa

Cikin ababen tarihin da suka taba faruwa a rana mai kamar ta yau zamu kawo muku takaitaccen tarihin yadda aka kashe Janar Murtala Muhammad, tsohon shugaban Najeriya a mulkin Soji.

An kashe Janar Murtala Muhammed a ranar 13 ga watan Fabrairun shekarar 1976.

Laftanar Kanal B Dimka shi ne ya jagoranci kisan tsohon shugaban kasar, wanda kuma ya samu hadin kan wasu manyan Najeriya da kuma kananan hafsoshin sojoji domin tsara juyin mulki.

A lokacin da aka kama Dimka kuma aka yanke masa hukuncin kisa, ya bayyana cewa tun a watan Janairun shekarar ta 1976 suka fara shirya makarkashiyar.

Sai dai kuma an samu nasarar murkushe juyin mulkin nasa inda aka yankewa Dimka da wasu mutane bakwai hukuncin kisa, kuma aka zartar da hukuncin a ranar 15 ga watan Mayu na shekarar 1976.

Leave a Reply