Qatar za ta kyautar wa Lebanon motocin da aka yi amfani da su a gasar Kofin Duniya

Qatar za ta kyautar da manyan motocin ɗaukar fasinja da aka yi amfani da su a gasar Kofin Duniya ga ƙasar Lebanon domin taimaka wa harkokin sufuri a ƙasar, kamar yadda kafar yada labaran Lebanon ta ruwaito.

Wasu majiyoyi sun ce firaministan ƙasar Najib Mikati ya tattauna batun da jami’an ƙasar Qatar bayan kammala gasar Kofin Duniya.

Hakan na zuwa ne bayan da hukumomin Qatar suka bayyana aniyarsu ta kyautar da wasu kayayyakin da ta yi amfani da su a lokacin gasar Kofin Duniya ga wasu ƙasashe masu tasowa.

Cikin abubuwan da Qatar ɗin ta ce za ta kyautar har da manyan filayen wasanni da aka yi amfani da su a lokacin gasar, da kujerun da ke filayen wasan, baya ga manyan motocin 1,000 da aka yi amfani da su wajen yin zirga-zirga da ‘yan kallo kyauta a lokacin gasar.

Leave a Reply