PSG na zawarcin Kane, Saudiyya na son Silva

A yanzu Harry Kane ne dan wasa lamba daya da Paris St-Germain ke son saye a bazaran nan mai zuwa bayan da Lionel Messi, ya tafi. (Le Parisien)

Dan bayan Ingila Kyle Walker, na son ci gaba da zama a Manchester City har ma ya fara tattaunawa kan hakan, duk da cewa Bayern Munich na sha’awarsa. (Mail)

Shi kuwa dan wasan tsakiya na Manchester City da Portugal Bernardo Silva, ya samu tayin zuwa gasar Saudiyya. (Athletic )

Marcus Rashford, na dab da kulla sabuwa kuma yarjejeniya ta tsawon lokaci a Manchester United. (Mail)

Dan gaban Jamus Kai Havertz ba shi da niyyar kulla sabuwar yarjejeniya a Chelsea, kuma daman Arsenal na sonshi. (ESPN)

Arsenal din ta bai wa dan wasanta na tsakiya na Ghana Thomas Partey, damar sauraren tayin tafiya gasar Saudiyya. (90min)

Mai tsaron ragar Everton da Ingila Jordan Pickford, na jin dadin zamansa a Goodison Park kuma babu wata maganar cewa Manchester United ta neme shi. (Mail)

Napoli na fatan cimma yarjejeniyar tsawaita zaman Victor Osimhen amma ta ce za ta saurari duk wani tayi mai karfi a kan dan Najeriyar a bazaran nan. (Metro)

Liverpool na son sayen matashin dan wasan tsakiya na Netherlands Ryan Gravenberch, mai shekara 21, daga Bayern Munich a bazaran nan. (Mirror)

Shi kuwa dan wasan tsakiya na Manchester City da Jamus Ilkay Gundogan, ya ce Borussia Dortmund ta tuntubi wakilinsa, amma ya ce batun komawa wasa Jamus ba ya cikin tsarinsa a yanzu. (Goal)

Chelsea na duba yuwuwar ko ta nemi damar sayen matashin dan wasan Senegal na gaba Nicolas Jackson, mai shekara 21, ta yuro miliyan 35 kamar yadda yarjejeniyarsa da Villarreal ta tanada. (ESPN)

Wasu bayanai na nuna cewa tsohon dan bayan Tottenham da Jamhuriyar Ireland Matt Doherty, wanda yanzu ba shi da kungiya na shirin tafiya gasar Saudiyya. (Sun)

Brighton na duba yuwuwar zawarcin dan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila Conor Gallagher. (Football Insider)

West Ham ba za ta samu damar sayen dan wasan tsakiya na Ajax da Mexico Edson Alvarez, ba amma kuma za ta ci gaba da zawarcin dan tsakiya na Fulham da Portugal Joao Palhinha. (Guardian)

Galatasaray na son sayen dan gaban Wolves Fabio Silva. Matashin dan wasan na Portugal mai shekara 20 ya yi zaman aro a kakar da ta wuce a Anderlecht da PSV Eindhoven. (Express & Star)

Leave a Reply