PSG na shirin kashe kuɗi kan Rashford, Felix ya yi kasuwa

Paris St-Germain na son mayar da ɗan wasan gaban Ingila Marcus Rashford ɗaya daga cikin ƴan wasan da aka fi biyan kuɗi a duniya a daidai lokacin da suke shirin sayensa, kwantiraginsa na daf da ƙarewa a Manchester United. (Mirror)

Kocin Manchester United Erik ten Hag ya ce kulob ɗin zai zaɓa ko ya tsawaita kwantiragin Rashford da ɗan wasan bayan Portugal mai shekara 23 Diogo Dalot har zuwa 2024 ganin cewa sun soma tattaunawa kan batun tsawaita kwantiragin ƴan wasan. (Metro)

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Brazil na shirin neman kocin Manchester City Guardiola domin gano ko yana son zama shugaban ƙungiyar ƙasar a ƙarshen kaka. (Sport – in Spanish) 

Chelsea da Manchester City da Manchester United duk sun bayar da buƙatunsu na ɗan wasan Croatia mai shekara 20 Josko Gvardiol sai dai kuma ita ma Bayern Munich na neman ɗan wasan bayan na RB Leipzig. (Foot Mercato – in French)

Wakilin ɗan wasan gaban Portugal Joao Felix wanda tuni ya soma tattaunawar farko da Chelsea da Manchester United na da burin magana da Aston Villa da Newcastle kan yadda suke son ɗan wasan na Athletico Madrid mai shekara 23. Spanish)

Arsenal da PSG duk sun shiga jerin kulob-kulob ɗin da ke neman Felix. (AS – in Spanish)

Akwai yiwuwar Juventus za ta iya sayen ɗan wasan Chelsea da Ingila Mason Mount mai shekara 23 da kuma barin ɗan wasan Faransa Adrien Rabiot mai shekara 27 tafiya, haka kuma kulob ɗin zai iya sakin ɗan wasan Argentina Leandro Paredes da na Amurka Weston Mckennie duk su tafi domin samar da kuɗin sayen ɗan wasan na Chelsea. (CalcioMercatoWeb – in Italian)

Shugaban Benfica Rui Costa ya ce kulob dinsa ba zai yarda duk wani ɗan wasan su ba ciki har da ɗan wasan Portugal mai shekara 21 Goncalo Ramos barin kulob ɗin har sai an cimma matsaya kan farashin sayar da su. Ana dai alaƙanta Ramos da tafiya Manchester United. (Correio da Manha – in Portuguese)

Leave a Reply