Our Programs

Tushen Rayuwa

Shirin da muka samar da shi domin bayani akan zamantakewar aure tsakanin ma’aurata da yadda zaman iyali zai kasance da kuma gina rayuwa mai inganci da albarka.

Shirin yana zuwa duk ranar Asabar karfe tara na dare (9PM) a maimaita ranar Litinin karfe tara na safe (9AM).

Latsa Nan domin sauraron shirin

 

Dalla Dalla

A wannan shiri muna duba ga alkawura da wakilan al’umma na siyasa suka dauka don bibiyar ko sun cika wadannan alkawura ko akasin haka. Yana zuwa ranar Laraba karfe goma na dare (10:00PM) a maimaita ranar Lahadi karfe takwas na dare (8:00PM).

Latsa nan Domin Sauraron Shirin

Arewa Ina Mafita

Shiri ne da yake tattauna matsalolin Arewacin Nigeria ta hanyar kallon yadda arewa take a da da kuma yadda take a yau domin samun matsalolin da ake fuskanta dakuma kawo mafita. Yana zuwa ranar Lahadi karfe goma na dare (10PM) a maimaita ranar Talata karfe shida na yamma (6PM).

Ke Duniya

Wannan shiri ne na musamman da muke kawo labarai na abubuwan al’ajabi da suke faruwa a cikin al’umma. Yana kawo muku labarai na ban ta’ajibi da mamaki.

Yana zuwa Litinin Zuwa Juma’a karfe tara na dare (9PM) a maimaita tara na safe (9AM).

Kasa Daya 

Shiri ne da yake kawo labaran abubuwan da suke faruwa a cikin al’umma. Yana zuwa Monday – Friday tara da rabi na dare 9-9:30PM sai maimaici tare da rabi na safe (9:30 AM.)

Naka Naka Ne

Shiri ne da yake duba ga kananan yara da nakasassu masu bukata ta musamman domin inganta rayuwarsu da ilmi. Yana zuwa duk ranar Talata a maimaita ranar Alhamis da karfe uku da rabi zuwa hudu na yamma (3:30-4:00PM)

Latsa Nan domin sauraron shirin

Jiya Ba Yau Ba

Shiri ne da ake gayyato dattijan mutane wadanda sukaga jiya kuma sukaga yau domin tattaunawa da su akan yadda jiya ta kasance domin shiryawa gobe. Yana zuwa ranar Laraba a maimaita ranar Asabar.

Hattara Matasa

Shiri ne da muke tattaunawa da masana akan matsalolin Matasa domin samun mafita da kuma kokarin kawo cigaba a tsakanin matasa. Yana zuwa duk ranar Laraba karfe biyu na rana (2PM) a maimaita ranar Asabar da karfe biyu na rana (2PM).

Tun Ran Gini…….

Shiri ne da yake Magana akan rayuwar yara da malamai da kuma mu’amalarsu. Da kuma daidaita fahimta tsakanin dalibai, malamai da iyaye domin samun ilmi mai inganci. Yana zuwa duk ranar Asabar karfe goma da rabi na safe (10:30PM).

Tsakar Gida

Shiri ne da yake tattauna matsalar auratayya domin samun gidaje da alumma na gari masu inganci. Shiri ne na kai tsaye yana zuwa ranar Talata karfe Tara na dare (9PM).

Barka da Warhaka

Shiri ne wanda masu gabatar da shirye Shirye wato DCA (Duty Continuity Announcers) suke yi tare da masu sauraro ta hanyar zabar batu su tattauna a kai. Yana zuwa kowace rana.

Zaben Guarantee

Shirin zabe domin sada zumunci inda masu sauraro suke sayen katin zabe da kuma mika gaisuwarsu ga yan uwa da abokan arziki. Yana zuwa ranar Litinin zuwa Juma’a karfe goma sha biyu da rabi na rana (12:30PM).

Mind your English

English teaching program aimed at helping the general public to improve their English Language including grammar and public speaking. The program comes every week Sunday from 10-10:30AM.

Fasahar Kirkira

Shiri ne da yake duba game da Fasaha da kirkira domin raino da kuma tallafar baiwa ta fasaha da kirkira. yana zuwa ranar Litinin da karfe hudu da rabi zuwa biyar na yamma (4:30-5:00PM).

Duniyar Kimiya

Shiri ne da yake duba tsakanin Kimiyar musulunci da Kimiyar zamani domin samun fahimta tsakanin Musulunci da Kimiya da kuma daidaita fahimta tsakanin fannonin biyu. Shirin yana zuwa ranar Talata karfe tara da rabi na dare (9:30PM) a maimaita ranar Asabar bakwai da rabi na dare (7:30PM).

Tambari

Wannan shiri ne wanda yake bayani game da Tarihin Kano da kuma masarautar kano. Yana zuwa muku kai tsaye ranar Talata da karfe goma na dare (10PM) sai a maimaita ranar Asabar takwas na dare (8PM).

Lafiya Don Mata

Shiri ne da yake kallon matsalolin mata kama daga ciki, haihuwa, raino da kuma kula da yaya. Shirin yana zuwa duk ranar Alhamis karfe hudu na yamma (4PM) a maimaita ranar Litinin karfe shida na yamma (6PM).

Da Kantar Zuci

Shiri na musamman da yake tattaunawa akan sana’o’i daban-daban musamman sana’o’in da maza ne kawai sukeyi amma a samu mata sunayi domin samun abin rufawa kai asiri.

Yana zuwa ranar Alhamis bakwai da rabi na safe (7:30PM) a maimaita ranar Litinin karfe hudu na yamma (4PM).

Adon Mace

Wannan shiri ne na koyar da girke-girke domin inganta rayuwar aure da kuma kyautata zaman iyali. Yana zuwa ranar Litinin karfe goma na safe (10:00 AM).

Kanun Jaridu (Papers Summary)

Shiri ne da yake kawo muku sharhin manyan jaridun Nigeria cikin Hausa domin tsokaci kan labarun da suka wallafa. Yana zuwa ranakun Litinin zuwa Juma’a kowane mako karfe takwas zuwa tara na safe (8-9AM).

News Bulletins

Wannan lokuta ne na labarai da muke gabatarwa a kowace rana cikin harshen Hausa da Turanci.

Labaran suna zuwa Karfe goma sha biyu (12 Noon), Karfe Uku na rana (3PM), sai kuma karfe bakwai na yamma (7PM) kai tsaye daga dakin watsa labarammu.

 

Abun Boye

Yana bankado wasu abubuwa da suka shafi Al’umma na boye a wasu hukumomi da kuma gayyato masu ruwa da tsaki domin fashin baki.

Yana Zuwa Ranar Alhamis karfe daya na rana (1PM) a maimaita ranar Litinin karfe goma na dare (10:00PM).

Labarin Wasanni

Shiri ne da yake kawo muku labaran wasanni kai tsaye daga dakin shirye-shiryemmu a dukkanin ranakun mako banda Juma’a da karfe goma sha daya zuwa sha biyu na rana (11-12PM).

 

Mu Tattauna

Wannan shiri ne na minti goma sha biyar wanda BBC Hausa suke tattaunawa akan matsasloli daban daban su kawo mana mu saka.

Yana zuwa ranar Asabar karfe uku da rabi na rana (3:30PM)

Taskar Muryar Amurka

Shiri ne da yake zuwa kai tsaye daga Muryar Amurka (VOA) wanda muke sakawa da karfe uku da rabi (3:30PM) na ranar Talata.

Dimokradiyya A Yau

Shiri ne da yake zuwa kai tsaye daga Muryar Amurka (VOA) kowace ranar Laraba da karfe uku da rabi na yamma (3:30PM).

Dandalin Nishadi

Wannan shiri ne na barkwanci wanda ya hada kabilu daban daban, Dan Gwari, Dan Buzu, Bafulatani sai Bahaushe da Bayerebe domin bada nishadi.

Yana zuwa ranar Laraba hudu da rabi na yamma (4:30PM) a maimaita ranar Lahadi uku da rabi na yamma (3:30PM).

Gamon Jini

Wannan shiri ne na karatun littafan SOYAYYA domin nishadantar da masu saurarommu musamman matasa maza da mata yana zuwa a ranar Litinin zuwa Juma’a karfe biyar da rabi na yamma (5:30PM) a maimaita karfe goma na safe (10:30PM).

Nishadin Zuciya

Shima wannan shiri ne na karatun littafan SOYAYYA domin nishadantar da masu saurarommu musamman matasa maza da mata yana zuwa a ranakun Asabar da Lahadi karfe biyar da rabi na yamma (5:30PM).

Taskar Nishadi

Shiri ne na kai tsaye tare da masu sauraro wanda yake basu damar zaben wakoki domin nishadantarwa da kuma amsa tambayoyi da basu kyauta. Yana zuwa karfe goma sha daya zuwa sha biyu na dare (11-12PM).

Likitan Masoya

Shirin da yake tattauna Nasarori da kalubale a duniyar masoya. Shirin da yake zuwa kai tsaye ranar Lahadi tara zuwa goma na safe (9-10AM) kowane sati.

Wasa Kwakwalwa

Kamar yadda sunan ya bayyana shiri ne tare da masu sauraro domin wasa kwakwalwa da kuma auna fahimtar masu sauraro da nishadantar da masu sauraro. Yana zuwa ranar Asabar Karfe hudu zuwa biyar na yamma (4-5PM).

Dausayin Yabo

Shiri ne da ake gayyato sha’irai wato makawan yabon Manzon Allah (SAW) domin hira da su a ranar Juma’a karfe hudu zuwa biyar na yamma (4-4:30PM).

Musics of All Class

Music session where we entertain our listeners with different songs.

Daga India

Shiri ne da yake kawo mana labaran abubuwan da suke faruwa a Bollywood kama daga labarai, Awards, Movies da sauransu. Yana zuwa kai tsaye ranar Alhamis karfe biyu na rana (2:00PM).

Yan Mazan Jiya

Shiri ne da yake gayyato tsofaffin Sojojin Nigeria domin hira da su don sanin yadda suka gudanar da yake yake.

Yana zuwa ranar Lahadi karfe hudu da rabi na yamma (4:30PM) a maimaita ranar Litinin karfe tara da rabi na safe (9:30AM).

Garkuwa

Wannan shiri ne na karatunn littattafan yaki domin koyarda jarumta da nishadi yana zuwa ranakun Laraba, Alhamis da Juma’a karfe tara da rabi na dare (9:30PM).

Majalisar Mata

Wannan shiri ne da mata zasu rinka tattaunnawa akan matsalolin mata ta hanyar barkwanci da nishadi. Zai rinka zuwa ranar Talata karfe Hudu na yamma (4:00PM).

Drama

Wasan kwaikwayo ne da zai rinka zuwa da hausa mai suna ‘KATANTANWA’. Zai rika zuwa ranar Lahadi karfe goma da rabi na safe (10:30AM) a maimaita ranar Talata hudu da rabi na yamma (4:30PM).

Tauraron Zamani

Wannan shirin ne da yake tattaunawa da mawaka yan film da duk wasu taurari a masana’antar Kannywood yana zuwa da karfe Shida zuwa bakwai na yammacin kowace Alhamis (6-7PM).

Yara Manyan Gobe

Tattaunawa game da rayuwar yara ta hanyar ilmantar da su. Makaranta ce a radio da take koyar da yara. yana zuwa ranar Juma’a karfe uku da rabi na yamma (3:30PM).

Lafiya Jari

Shiri ne da yake tattaunawa da likitoci akan cututtuka daban-daban tare da ziyartar Asibitoci don ganin halin da suke ciki da kuma tattaunawa da masara lafiya akan korafe korafe da suke fuskanta domin isarwa ga gwamnati. Yana zuwa  a ranar Laraba uku da rabi na yamma (3:30PM) a maimaita Lahadi karfe hudu karfe hudu na yamma (4:00PM).

Lafiya Don Mata

Shirin yana gayyatar Likitoci domin tattaunan  cututtukan mata kamar ciki, haIhuwa da raino da sauran cututtuka na mata da kananan yara. Yana zuwa ranar Alhamis karfe hudu zuwa biyar na yamma (4-5PM) a maimaita ranar Litinin karfe Shida zuwa bakwai na dare (6-7PM).

Musulunci da Rayuwa

Shiri ne da yake bayanin yadda rayuwar musulmi zata kasance bisa tsari na shari’a ta fuskar tarbiya, mu’amala da sauran kyawawan halaye.

Yana zuwa duk ranar Laraba karfe hudu na yamma (4PM) a maimaita ranar Juma’a karfe bakwai da rabi na dare (7:30PM).

Al Lu’u Lu’u Wal Marjan

Karatun Littafin Hadisai wanda Malam Lawan Abubakar Shu’aibu Chief imam na Masallacin Juma’a na Triumph yake gabatarwa. Yana zuwa ranar Laraba karfe tara da rabi na safe (9:30AM).

Hasken Annabta

Shiri ne da yake duba ga sakon da Annabawa suka zo da shi na shiriya domin fuskantarsa da kuma dora al’umma kan hanyyar shiriya. Yana zuwa ranar Juma’a da karfe shida na yamma (6PM) a maimaita ranar Lahadi karfe bakwai da rabi na dare (7:30 PM)

Mace Ta Gari

Shiri ne na addinin musulucin da yake kawo siffofin mace ta gari domin kyautata rayuwar mata. Yana zuwa ranar Talata karfe daya na rana (1PM) sai a maimaita ranar Juma’a karfe shadaya na safe (11PM).

Tarbiya A Musulunci

Shiri ne da bayanin yadda tarbiyar yara take a musulunci domin gina al’umma ingantacciya  da kuma taimakawa iyaye wajen gina tarbiyar yara. Yana zuwa kai tsaye ranar Litinin karfe daya zuwa daya daya da rabi (1-1:30PM) a maimaita ranar Lahadi tara na dare (9PM).

Gwadaben Tsira

Yana zuwa ranar Asabar karfe daya na rana (1PM) a maimaita ranar Laraba da karfe daya na rana shima (1PM).

Ibada a Aikace

Shiri ne da yake bayani yadda ake gudanar da ibadu na addinin musulunci a aikace kamar tsarki, alwala sallah da sauransu. Yana zuwa ranar Alhamis tara da rabi na safe zuwa karfe goma (9-10PM).

Tafsir and Hadith

  1. Tafsir Mufti Menk Litinin karfe hudu ziwa biyar (4-5PM)
  2. Tafsir Sheik Ibrahim Daurawa
  3. Tafsir Malam Nasidi Abubakar G/Dutse
  4. TafsirSheik Ibn Uthman
  5. Tafsir Malam Ibrahim Khaleel
  6. Tafsir Sheik Isa Waziri
  7. Riyaddussalihin
  8. Umdatul ahkam
  9. Khudba Alfurqan