Osinbajo zai tafi Vietnam domin ƙulla hulɗar kasuwanci

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, zai yi tafiya zuwa ƙasar Vietnam domin tattauna batun hulɗa kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.

A wata sanarwa da babban mai taimaka masa kan kafofin yada labarai Laolu Akande ya fitar ya ce a yayin ziyarar mataimakin shugaban ƙasar nan zai gana da shugaban ƙasar ta Vietnam da mataimakin shugaban da firaminista tare da wasu jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa na kasar.

Sanarwa ta ce ziyarar  ta kwanaki biyar da mista Osinbajo zai yi na zuwa ne bayan da mataimakin firaministan Vietnam Vuong Hue ya ziyarci Najeriya a watan Oktoban 2019 domin duba hulɗar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.

Leave a Reply