Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana tsayawa takarar ce a wani jawabi ta bidiyo da aka yada ta talbiji da sauran kafofin sada zumunta inda ya yi bayanin irin abubuwan da zai yi idan ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari.
Ya ce yana neman tsayawa takarar ce domin inganta rayuwar ‘yan kasar yana mai cewa a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa yana da kwarewar shugabancin Najeriya.
“A cikin shekara bakwai, na bauta wa gwamnati a matakai daban-daban, kuma bisa umarnin shugaban kasa, na wakilci kasar nan a muhimman bangarori a kasashen waje. Na ziyarci kusan kafatanin kananan hukumomin Najeriya. Na je kasuwanni, da masana’antu, da makarantu da gonaki,” in ji Farfesa Osinbajo.
Ya kara da cewa ya je gidajen talakawan kasar a yankuna daban-daba, sannan “na tattauna da kwararru a bangaren fasaha a Lagos, Edo, da Kaduna; da kuma taurarin Nollywood da Kannywood; da mawaka daga Lagos, Onitsha, da kuma Kano. Kuma na yi magana da kanana da manyan ‘yan kasuwa”.
Mataimakin shugaban na Najeriya ya ce ya samu wannan kwarewa ce domin ta zama silar fahimtar matsalolon Najeriya da kuma yadda zai magance su.
Baya ga kewaya da zai yi jihohi domin neman magoya baya, ‘yan kwamitin yakin neman zaben sa za su shirya kuri’ar jin ra’ayin jama’a domin tattara shawarwari game da matakin da ya dauka na tsayawa takarar a zaben 2023.
Ana ganin Farfesa Osinbajo zai samu magoya baya, amma yadda zai bullo a siyasance ya kalubalanci manyan masu sha’awar takarar biyu Bola Tinubu da Mr Rotimi Amaechi, shi ne abin jira a gani.
Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya gabatar da jawabi ga wani taron jama’a inda ya kaddamar da manufarsa ta tsayawa takara kamar yadda tsohon gwamnan jihar Rivers, kuma ministan sufuri Rotimi Amaechi ya yi a Fatakwal a ranar Alhamis din da ta wuce.
Shi kuwa tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan Ebonyi David Umahi, su sun yi bayani ne ga ‘yan jarida a lokacin kaddamar da takarar tasu, bayan sun gana daban-daban da Shugaba Buhari.
Rahotanni sun ce kafin sakin bidiyon da za a yi a ranar Litinin, sai da Mr Osinbajo, ya yi buda baki tare da gwamnonin jam’iyyar APC a gidansa.
Tuni dai Osinbajo ya bude ofishin kamfen dinsa a Wuse da ke Abuja.