Mai bai wa Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, shawara kan harkokin siyasa ya ce suna fatan Bola Ahmed Tinubu zai ci girma ya bar wa mai gidansu takarar shugaban ƙasa a inuwar jam’iyya mai mulki ta APC saboda ya fi shi cancanta.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jagoran APC na ƙasar ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takara kuma yake ci gaba da ziyartar muhimman mutane don neman goyon baya.
Mataimakin shugaban wanda yaron siyasar Bola Tinubu ne amma ana ganin alamun cewa shi ma yana sha’awar tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2023.
Mai ba mataimakin Shugaban shawara Abdurrahman Baffa Yola, ya shaida wa BBC cewa Osinbajo, mutum ne mai sha’awar ci gaban kasarsa.
Ya ce,”Bisa la’akari da yadda mataimakin shugaban Najeriyar ke kishin kasarsa, to idan har aka bashi damar kasancewa shugaban kasar to ko shakka ba bu zai yi wa kasarsa aiki”.
Abdurrahman Baffa Yola, ya ce” Ba wai Osinbajo ya bayyana cewa yana son takarar shugabancin Najeriya bane, to amma mu da muke aiki tare da shi muna karbar sakonni a kullum, kuma muna ganin yadda kungiyoyi ke kira gareshi da ya tsaya takarar”.
Ya ce, har yanzu Osinbajo bai furta cewa zai tsaya takarar ba, aikin da aka dora masa shi ne a gabansa a ko da yaushe.
”Dangane da yadda zata kasance tsakanin mataimakin shugaban Najeriyar da kuma Bola Ahmed Tinubu, wanda uban gidansa ne kuma ya fito ya nuna sha’awar sa ta fitowa takarar shugaban kasa, mu zamu barwa lokaci, amma kuma shi kansa Tinubun ya san nagartar Osinbajo”.
Ya ci gaba da cewa “Mu muna ganin nagartar Osinbajo ta fi ta Tinubu, kuma muna sa ran idan har mataimakin shugaban kasar ya amsa kiraye-kirayen da ake masa na tsayawa takarar shugaban kasa, to shi kansa Tinubun zai iya cin girma ya bar kaninsa”.
Mai bai wa mataimakin shugaban Najeriyar shawarar ya ce ”ba wai mu kadai ne muke ganin cancantar Osinbajo ba, idan aka yi la’akari da gogewarsa da iliminsa, za a iya cewa ba bu wanada ya zama ya kai shi gogewa da kuma cancantar tsayawa takarar shugaban Najeriya a jam’iyyar APC.