NUJ tayi Allah-wadai da farmakin da aka kaiwa wakilin Jaridar Leadership a Kano.
Kungiyar yan jaridu ta kasa reshan jihar Kano, ta bayyana rashin jin dadinta kan abinda ya faru yayin wani taron manaima labarai a gidan dan majalisar Tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Tudunwada da Doguwa Hon. Alassan Ado Doguwa na zargin Dan majalisar da kaiwa wakilin jaridar Leadership Abdullahi Yakubu farmaki ta hanyar cin zarafinsa.
Duk duk da cewa batun yana gaban kotu da kuma jami’an yansanda; kungiyar ta NUJ ta nuna fatanta na ganin an gudanar da bincike na hakika dan kwatarwa Dan jaridar hakkinsa a matsayinsa na dan kasa mai cikakken yanci.
A wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar yan jaridu ta kasa reshen jihar Kano Comerade Abbas Ibrahim da Sakataren Kungiyar Abba Murtala sun bukaci samun dorewar kyakkyawar alaqa tsakanin Gwamnatin Kano, Yan siyasa da ‘yan jaridu ba tare da kyara ko tsangwama ba.