NLC da TUC Sun Janye Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

Janye Yajin Aikin Ya Biyo Bayan Cimma Yarjejeniya Da Sukai Da Gwamnati A Wata Ganawar Kimanin Sa’o’i Biyar A Daren Ranar Litinin 03-06-2024, Inda Gwamnatin Tarayya Ta Amince Zata Biya Sama Da Dubu Sittin N60000 Na Mafi Karancin Albashi .
Shugaban Kungiyar Kwadago NLC Joe Ajaero Ya Sanar Da Janye Yajin Aikin Na Kwanaki 5 Inda Zasu Cigaba Da Tattaunawa Da Wakilan Gwamnati Har Na Tsawon Mako Daya Domin Cimma Cikakkiyar Matsaya Ka Batun Mafi Karancin Albashin.
Tin A Farko Kungiyoyin Kwadagon Sun Zargi Gwamnati Da Gaza Cika Alkawari, Wanda Tin A 31 ga Watan Mayun Da Ya Gabata Gwamnatin Tace Zata Yi Karin Mafi Karancin Albashin, Amma Ta Gaza Yin Hakan, a Cewar Ajaero.
NLC da TUC Sun Bukaci Gwamnatin Tayi Karin Mafi Karancin Albashi na N49000.

Leave a Reply