Nisan makaranar firamare daga ƙauyenmu ya sa yaranmu ba sa karatu

Babban abin da ke damun mutanen ƙauyen ‘Yanbita da ke gundumar Borindawa a ciki ƙaramar hukumar Malumfashi shi ne rashin makarantar firamare a ƙauyen nasu .

Yaran ƙauyen kan share tafiya mai nisa kafin su kai ga inda makarantar firamaren take.

Baya ga nisa kuma mutanen ƙauyen sun koka cewa akwai babbar hanyar mota da ta tashi daga Funtua zuwa Kano, wadda hanya ce mai cike da zirga-zirgar ababen hawa.

”Kuma hakan yana matuƙar yin barazan ga ƙananan yaranmu waɗanda ba su mallaki hankalinsu ba”, in ji Ibrahim Haruna Saleh.

Hakan ne ma ya sa da yawa daga cikin yaran ƙauyen ba sa zuwa makarantar Furamare, ga waɗanda suke zuwa ma kuma wasu da dama sun daina zuwan bisa waɗannan dalilai. 

Ibrahim wanda mazaunin ƙauyen ne, ya kuma shaida wa BBC cewa a baya akwai wata makarantar furamare ta wucin-gadi da yaran nasu ke zuwa.

To amma a cewarsa da aka tashi gina makarantar sai aka tafi wani waje mai nisa.

”Da tafiyar ba ta da nisa daga ƙauyenmu zuwa inda take to amma da aka tashi gina ta sai aka tafi wani waje mai nisa kasancewar a can aka samu wuri”, in ji Ibrahim Haruna Saleh.

Ya ci gaba da cewa ”baya ga nisan sabuwar makarantar, dole sai yaran nasu sun tsallaka babban titin Funtua zuwa Kano kafin su isa makarantar, kuma yara ne ƙanana waɗanda shekarunsu suka kama daga bakwai zuwa sama”,

Domin kuwa a cewarsa an sha samun matsaloli sakamakon wannan hanya.

‘Ɗalibai kan yi tafiyar kilomita ɗaya zuwa biyu’

Iyayen yaran wannan ƙauye sun koka game da irin doguwar tafiyar da yaransu ke yi a ƙafa kafin su kai ga inda makarantar take.

A cewarsu a baya sun saba yaransu ba sa wata tafiya mai nisa kafin su isa makarantar da suke, wacce ke cikin makarantar Kurame ta Malumfashi.

To amma a yanzu yaran nasu kan yi tafiyar kilomita ɗaya da rabi zuwa biyu kafin su isa inda sabuwar makarantar take, kamar yadda Maiunguwan ƙauyen ya shaida wa BBC.

Mai unguwar ƙauyen ya shaida wa BBC cewa makarantar ta kwashe kusan shekara 10 a cikin makarantar Kuramen, to amma kwatsam, sai a bara aka ɗauke ta aka ƙara mata nisa, tare da mayar da ita wani waje a cikin garin Malumfashi.

‘Mota ta taɓa buge ɗana a hanyar zuwa makaranta’

Wani Uba ya ce ya cire ‘yarsa daga makarantar saboda nisan da makarantar ke da shi, kasancewarta mai ƙananan shekaru.

Ya ƙara da cewa ”ga kuma matsalar motoci sun yi yawa a titin, kuma dole sai sun ƙetare titin kafin su isa makarantar”

Mallam Mansur Lawan ‘Yanbita wanda shi ma mahaifin yara ne ya ce sakamakon ɗauke makarantar daga inda suka saba da ita ya sanya su cikin fargabar ababen hawa.

Ya ƙara da cewa ”Hatsarin mota ya taɓa rutsawa da yarona guda ɗaya, dalilin da ya sa a yanzu a duk lokacin da ban samu sukunin kai yarana makaranta da kaina ba, to a wannan rana sukan zauna a gida”.

Tafiya ce mai nisan kilomita ɗaya da rabi zuwa biyu, daga ƙauyen na ‘Yanbita zuwa Malumfashi inda makarantar Furamaren take, kuma dole sai an tsallar babbar hanyar Funtua zuwa Kano.

Hanya ce mai cike da zirga-zirgar ababen hawa kamar yadda Malam Usman Musa mai unguwar ƙauyen ya shaida wa BBC.

Leave a Reply