Ni ne dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a Taraba — Sanata Bwacha

A jihar Taraba da ke arewa maso gabashin kasar, dan takarar gwamna a jam’iyyar APC na jihar ya fito ya yi watsi da rade-radin da ake cewa jam’iyyar bata da dan takarar gwamna.

Sanata Emmanuel Bwacha, ya shaida wa BBC cewa shi ne dan takarar gwamna a jihar, kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da ma kotu sun san cewa shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar APC.

Sanata Bwacha, ya ce rigingimun da suke a jam’iyyar ta APC sun kai ga sun je kotu kala-kala, har aka dawo aka yi zabe na biyu bayan na farko da babbar kotun Jalingo ta rushe tace a sake yin zabe.

Ya ce,” Bayan na sake zabe kamar yadda kotu ta bayar da umarni, na sake samun nasara ta zama dan takarar gwamna a APC.”

Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Taraba ya ce ita kanta hukumar INEC, ta ce bata fitar da sunansa a matsayin dan takara ba.

Sanata Bwacha, ya ce,” Kotu ta ambata cewa ni Sanata Emmanuel Bwacha, ni ne dan takarar gwamna a APC, kuma INEC ta san da haka.”

Ya ce, ‘’ Su masu yada rade-radin cewa babu dan takarar gwamna a APC, ba zasu gaji da karya ba saboda abin da suka gada ke nan saboda idan basu yi haka ba sun san sun fadi zabe, kuma idan sun yi hakan suna yi ne don su rikitar da magiya bayanmu su kuma sanya musu shakku a zukantansu.”

Sana Bwacha, ya ce su da kansu sun san cewa shi ne da n takarar jam’iyyar amma kuma d ayake anjima ana kara a kotu shi yasa suka wannan rade-radi.

Ya ce, ‘’ Kafin lokacin zabe za muyi kokari mu fahimtar da mutanenmu saboda mun san su, sannan kuma duk wanda ya kawo wata magana zamu ce yaje INEC ya tambaya ko ya duba yaga waye dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a Taraba.”

Sanata Bwacha, ya ce yana kir aga magiya bayansu da kada su yarda da jita jitar da ake na cewa babu dan takarar gwamna a APC, karyace kawai.

Wannan danbawar dai na zuwa ne a yayin da ya rage kasa da mako da guda a gudanar zaben gwamnoni da na ‘yan majilisun jihohi a Najeriya.

Leave a Reply