N’Golo Kante, na son zama a Chelsea, Everton ta soma tattaunawa da Alex Iwobi kan sabon kwantiragi

Atletico Madrid ta nuna sha’awar sayen ɗan wasan gaba na Brazil da Liverpool, Roberto Firmino. (Todo Fichajes – in Spanish)

Leicester City na sa rai kan ɗan wasan tsakiya na Manchester United da Netherlands Donny van de Beek, 25. (Ekrem Konur)

Ɗan wasan gaban Brazil Gabriel Martinelli, mai shekara 21, ya ce yana son ƙulla sabon kwantiragi da Arsenal kuma yana tattaunawa kan ruɓanya albashinsa na kusan £50,000 kowanne mako. (Times – subscription required)

Brentford na shirin miƙa wa Ivan Toney mai shekara 26 sabon kwantiragi domin janye shi daga rige-rigen da Manchester United, Leeds, Newcastle da West Hamke yi. (Mirror)

Everton ta soma tattaunawa da ɗan wasan tsakiya a Najeriya, Alex Iwobi kan wata sabuwar kwantiragi. (Football Insider)

Dan wasan tsakiya a Faransa, N’Golo Kante, 31, na son ci gaba da zama a Chelsea duk da alakanta shi da Paris St-Germain. (Le10 Sport – in French)

Leave a Reply