NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar watan Nuwamban 2022

Hukumar shirya jarrabawar Najeriya, NECO, ta fitar da sakamakon jarrabawar da aka yi ta watan Nuwamba da Disamba na 2022 ta daliban manyan makarantun sakandire.

Shugaban hukumar Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, shi ne ya sanar a Minna, babban birnin jihar Naija.

A bayanin da ya yi, ya ce a jumullar dalibai 59,124 suka yi jarrabawar, daga cikinsu 31,316 maza ne waɗanda yawansu shi ne kashi 52.96 cikin ɗari.

Yayin da mata suka kasance 27,808, kashi 47.03 cikin ɗari.

Farfesa Wushishi ya ƙara da cewa daga cikin yawan ɗaliban da suka rubuta jarrabawar harshen Ingilishi 58,012 guda 44,162, wato kashi 76.13 cikin ɗari sun samu kiredit zuwa sama.

Yayin da ɗalibai 57,700, da suka yi jarrabawar lissafi guda 43,096, wato kashi 74.69 cikin ɗari suka ci kiredit zuwa sama.

Shugaban ya ƙara bayani da cewa yawan ɗaliban da suka ci kiredit biyar zuwa sama a duka jarrabawar da ta haɗa da Ingiishi da lissafi 33,914 wato kashi 57.36 cikin ɗari.

Hukumar ta NECO, wadda ta fitar da sakamakon jarrabawar bayan kwana 57, ta kuma ce an samu dalibai 11,419 da laiffukan da suka danganci satar jarrabawa, saɓanin 4,454 da aka kama 2021, wanda hakan ta ce ya nuna ƙaruwar matsalar sosai.

Leave a Reply