NDLEA Ta Lalata Tan 24 Na Miyagun Kwayoyi A Kwara

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA, ta lalata miyagun kwayoyi da nauyinsu ya kai sama da tan 24 da ta kama a Jihar Kwara.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, ya ce, NDLEA ta yi wannan aikin ne a Ilorin.

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yaba wa hukumar da wannan nasarar da ta samu a jihar.

AbdulRazaq ya bai wa NDLEA tabbacin gwamnatinsa za ta ci gaba da mara mata baya don ci gaba da aikinta a jihar yadda ya kamata.

A nasa bangaren, Kwamandan Hukumar ta NDLEA a jihar, Ibrahim Saidu, ya ce, sun samu nasarar gurfanar da dillalan miyagun kwayoyi mutum 171 a jihar a cikin wannan shekara.

Leave a Reply