Hukumar hana sha da fatauchin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar kogi, tayi nasarar kwace kayan mayen da nauyin su yakai kilogram dubu 5o da 6.
Kwamandan hukumar ta jihar Mista Alfred Adewumi ya ce, sun kwace wadannan adadin ne a tsakanin shekarar 2020 zuwa watan satumbar shekarar 2021 , sakamakon zagayen ran gadi da bsuke yi a jihar.
Mista Adewumi ya bayyana hakan ne a lokachin da ake gudanar da wani taro ,wanda akaiwa take da Yaki da taamalli da miyagun kwayoyi, hadi da karawa wasu daga cikin jamian hukumar guda 18 matsayi a jihar .
Daga bisani ya bayyana dalilin da yasa akafi samun kasuwanchin kayan maye a jihar ta kogi ,in day ace ana kasuwanchi kayan maye a kasuwae Ogbugwu Dake Onitsha ,da kuma samar dasu a wasu maaikatu a jihohin Anambra ,da Delta ,wanda kuma duk makwabtane da jihar ta su, yana mai cewa hakan ya saka jihar tasu a halin tsaka mai wuya.