NDLEA ta kama mutum 192 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi

Hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi ta kasa – NDLEA, ta kama wasu mutane 192 da ake zargi da safarar kwayoyi tsakanin watan Janairu zuwa Satumba a jihar Ebonyi.

Hukumar ta kwace kwaya da ta kai kilogiram 113 a jihar, kamar yadda kwamandan hukumar Iyke Uche, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa.

A bangaren safarar kwayoyi, babban kwamandan ya ce ba a fiye kasuwancin kwayoyi a jihar ba, kawai dai tana da masu ta’ammali da ita ne da yawa.

Leave a Reply