Najeriya za ta faɗa cikin matsalar abinci a 2023, in ji IMF

Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF, ya ce Najeriya na fuskantar barazanar faɗawa cikin matsalar abinci a 2023, saboda hauhawar farashi da kuma ambaliyar ruwa da tsadar taki.

A cewar kiddidiga hukumar NBS, hauhawar farashi a Najeriya ya kai sama da maki 23 cikin 100 a watan Oktoban 2022, yayin da farashin wasu kayayyakin abinci ya karu daga kashi 50 zuwa 100.

Sannan rahoton IMF ya ce duk da irin wadannan matsaloli, akwai kuma yakin Ukraine da ke shafar tattalin arziki da farashin kayan abinci.

A makon da ya gabata ne hukumar kididdiga ta kasa a Najeriya ta ce ‘yan kasar nan miliyan 133 ke cikin talauci, kuma galibinsu ba sa samun ilimi da tsaro da kulawar lafiya.

Leave a Reply