Najeriya za ta ci gaba da kwase ‘yan ƙasarta da ke Sudan a yau Asabar

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya da ta Jin-ƙai da agajin gaggawa sun ce a yau Asabar motoci 29 za su isa Sudan domin kwaso sauran ɗalibai da sauran ‘yan Najeriya da suka rage a ƙasar.

Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, ma’aikatun sun yi ƙarin haske kan halin da ake ciki game da ɗaliban Najeriya da rikicin Sudan ya rutsa da su.

Sanarwar ta shawarci waɗanda za a kwaso su tsaya a inda aka umarce su da kayan da za su iya riƙewa a hannu kawai, kada su yi amfani da irin abubuwan da suke yawo a kafafen sada zumunta.

Sanarwar ta ce wakilan ofishin jakadancin Najeriya za su kasance a Khartoum domin tabbatar da an kwashe ɗaliban da sauran ‘yan Najeriyar da ke birnin.

An kuma shawarce su da su tanadi takardunsu na fita daga ƙasar, ta yadda idan sun je iyaƙar Aswan ta Masar ba za a sha wuyar tantance su ba.

Tun da fari sanarwar ta ambato cewa an kwaso mutum 637 daga Khartoum cikin motoci 13, waɗanda ta ce a halin da ake ciki suke kan iyakar Masar ana tantance su.

Gabanin wannan sanarwa, hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce daga safiyar Juma’a ne za a fara kwaso ɗaliban ƙasar da ke karatu a Sudan bayan sun isa Aswan a cikin ƙasar Masar.

Kuma jirgin saman Air Peace da zai yi aikin kwashe ɗaliban da sauran ‘yan Najeriya, zai tashi da ƙarfe 6 na yamma zuwa Aswan, cewar shugaban hukumar ba da agajin gaggawar.

To sai dai har yanzu ba a ji ɗuriyar jirgin ba, abin da ya sanya iyaye da sauran al’ummar ƙasar cikin damuwa.

Leave a Reply