Najeriya ta ja kunnen ƴan ƙasarta masu tafiya turai

Gwamnatin Najeriya ta fitar da wasu shawarwari ga al’ummarta masu zuwa ƙasashen Amurka da na Tarayyar Turai.

A wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja, ministan yaɗa labarai na Najeriya Lai Mohammed ya ce an fitar da shawarwarin ne bayan rahotanni na kai wa ƴan Najeriya hari da ƙwace masu kaya a ƙasashen waje, ciki har da birnin London.

Mohammed ya ce ana karɓe wa mutanen da suka fito daga Najeriya kaya, ciki har da kuɗi da fasfo na tafiye-tafiye.

Saboda haka ya ce ya kamata ‘ƴan Najeriya da ke tafiye-tafiye zuwa ƙasashen nahiyar Turai da Amurka su rinƙa yin taka-tsantsan. A kwanakin baya ne ƙasashen Amurka da Birtaniya da kuma wasu kasashen na daban suka gargaɗi al’ummarsu kan zuwa Najeriya saboda rashin tsaro da ake fama da shi

Leave a Reply