Najeriya Na Asarar sama da Naira Biliyan 4 Duk Shekara Kan Rikicin Manoma Da Makiyaya

Kungiyar Mercy Corps mai bada agaji kan al’amuran da suka shafi tattalin arziki da tsaro ta kasa da kasa, ta koka a kan yadda rikice-rikicen manoma da makiyaya a kasar nan ke yawan afkuwa.

Daraktan kungiyar a Najeriya, Ndubisi Anyanwu ne ya sanar da hakan; a hirarsa da manema labarai a Jihar Kaduna, jim kadan bayan kammala wani taron masu ruwa da tsaki da kungiyar ta gudanar a jihar.
Ya ce, kungiyar ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki ne a karkashin tallafin USAID.
Anyanwu ya kara da cewa, wannan rikici na manoma da makiyaya na jawo wa Najeriya tabka asarar sama da Naira biliyan 4 a duk shekara.
Daraktan ya ci gaba da cewa, daukar matakan gaggawa kan wannan rikici da ke faruwa a tsakaninsu; shi ne kadai mafita ga zaman lafiyar Najeriya.

Leave a Reply