Najeriya: Ba a biyan mu alawus — Masu tsaron iyaka

Jami’an tsaron da ke aiki na musamman don kula da iyakokin Najeriya wajen hana satar shigar da haramtattun kaya, sun koka a kan rashin biyan su kuɗaɗen alawus-alawus na aiki.

Ma’aikatan sun koka ne tare da yin kira ga waɗanda lamarin ya shafa a kan su taimaka a biya su haƙƙoƙinsu.

Ɗaya daga cikin ma’aikatan da BBC ta tattauna da shi amma ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, suna wahala ƙwarai da gaske a aikin.

Jami’in ya ce, ma’aikatan da ke aiki a tsare iyakokin Najeriyar don sanya idanu da hana shigar da haramtattun kaya da mutane ba bisa ƙa’ida ba, sun haɗar da sojoji da jami’an hukumar hana fasa-ƙwauri da jami’an shige da fice da kuma na hukumar ‘yan sandan farin kaya wato DSS.

Ya ce, “ Muna wahala sosai a wannan aiki da muke yi na shugaban ƙasa, don har yanzu ba a biya mu ba, (tsawon) shekara ɗaya da wata hudu kenan.”

Jami’in ya ce, lokacin da suka fara aikin, Marigayi Abba Kyari da Hamidu Ali, shugaban hukumar hana fasa-ƙwauri, sun tsaya tsayin daka wajen ganin ana biyan su haƙƙoƙinsu duk wata.

Ya ce, ‘’ Duk da an dakatar da biyan mu (kuɗaɗen) alawus ɗin tsawon waɗannan watanni ba mu daina aikin da aka sa mu ba, na ganin cewa ba a shiga da kayan da gwamnati ta haramta cikin Najeriya.”

Ya ce, “ Wasu sun mutu a cikinmu, an kashe wasu, ba kuma abin da aka yi wa iyalansu, gaskiya muna cikin wahala.”

Ma’aikacin ya ce, sun sha kai kokensu ga waɗanda suka kamata, amma babu abin da aka yi, sai dai cewa za a yi kawai a baka.

“Abin takaicin ma, idan mutum ya fiye magana a kan batun haƙƙinsa sai a ce za a kore shi daga aiki.”

Ya ce, ”A gaskiya mun yi wa gwamnatin Buhari adalci, don haka mu ma ya kamata a yi mana adalci, saboda ba mu gaza wajen sauke nauyin da aka ɗora mana ba.”

“Tsare (iyakokin) ƙasa da muke yi, muna tare da sojojin Nijar da sauransu, sai dai mu ga su ana biyan su amma mu ko oho sai tsabar wahala da muke sha,” in ji shi.

Don haka, “Muna kira ga shugaban ƙasa da mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro da kuma shugaban hukumar hana fasa-ƙwauri su taimaka a biya mu haƙƙoƙinmu na tsawon watanni”.

“Fargabarmu ita ce ga shi Shugaba Buhari ya kusa sauka, ba mu sani ba, ko idan wanda ya hau zai biya mu ko a’a.”

Ma’aikacin ya ce idan gwamnati ba ta gamsu da aikin da suke yi ba ne, dalilin da ya sa aka daina biyan su alawus, to ya kamata a sallame su daga aikin.

Leave a Reply