Na Tabbata Tinubu Zai Kai Najeriya Tudun-Mun-Tsira —Aisha Buhari

Aisha ta ce hangen nesan, iya siyasa da kyakkyawan aniyar Tinubu ga Najeriya za su kai kasar ga nasara

Matar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta ce tana da yakini cewa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, zai jagoranci Najeriya zuwa tudun-mun-tsira, saboda hangen nesansa da gogewarsa a siyasa.

Aisha Buhari ta ce da wadannan siffofi da kuma kyakkyawan kudurin da na Tinubu yake da shi ga daukacin al’ummar kasar ba tare da wani bambaci ba, sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasararsa a zaben da aka kammala.

Ta bayyana haka ne a sakon taya murna ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, bisa nasarar da ya samu a zaben da aka kammala.

Aisha Buhari, ta kuma taya zababben mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, murnar cin zabe.

Ta kara da cewa, “Ina taya murna ga matar zababben shugaban kasa kuma ’yar siyasa, Sanata Oluremi Tinubu, wadda ba na shakkar cewa matan Najeriya za su more a karkashin gwamnatinku.”

Aisha Buhari ta bayyana godiyarta ga Allah Madaukakin Sarki da aka gudanar da zaben cikin nasara, sannan ta jinjina wa ’yan Najeriya da suka fito suka kada kuri’a kuma aka ba su abin da suka zaba.

Leave a Reply