Mutum tara sun mutu a tagwayen harin bom a Somaliya

Akalla mutum tara ne suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata a wasu tagwayen hare-haren bom da aka kai tsakiyar Somaliya.

Rahotonni sun ce an kai harin ne da ƙananan motoci da sanyin safiyar ranar Laraba a garin Mahas.

To sai dai an samu rahotonni masu cin karo da juna game da inda aka nufa da harin.

Wani shafin intanet da ke da alaƙa da ƙungiyar al-Shabab ya ce sojojin Somaliya aka nufa da harin, inda wani shafin intanet mai zaman kansa ke cewa an kai harin ne kan wani gidan abinci, a yayin da kafar yaɗa labaran gwamnati ke cewa an kai harin ne kan shagunan fararen hula.

Jami’an tsaro na gudanar da bincike game da lamarin.

Leave a Reply