Mutum shida sun mutu tara sun jikkata a haɗarin tirelar albasa da bas a Kwara

Mutane shida sun rasa ransu tara kuma suka jikkata a wani haɗarin mota da ya auku a Jihar Kwara, a kan titin Ganmo da ke yankin ƙaramar hukumar Ifelodun a jiya Laraba.

Bayanai sun nuna cewa haɗarin ya faru ne tsakanin wata motar bas ta haya kirar Suzuki, mai lamba BDJ-134XB da kuma wata tirela shuɗiya, ƙirar DAF mai lamba ABC435XN, wadda ta taso daga Jihar Sokoto, da albasa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Wasu sun ce tirelar ce ta ƙwace wa direbanta saboda gudun da yake yi ta kara wa bas ɗin.

Jaridar ta ce a tattaunawar da ta yi da shugaban hukumar kiyaye haɗura ta ƙasar (FRSC), a jihar Frederick Ogidan, ya tabbatar da aukuwar haɗarin.

Sannan ya ce wasu mutanen tara sun ji raunuka kuma ana yi musu magani a asibiti, yayin da aka ajiye gawarwakin waɗanda suka rasun a asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan (UITH, Oke-Oyi).

Leave a Reply