Mutum shida sun mutu a wani hadarin mota a Bauchi

Hukumar kiyaye afkuwar haɗura a Najeriya ta ce mutum shida ne suka mutu yayin da biyu suka samu rauni a wani haɗarin mota da ya afku a ƙauyen Dinki da ke jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Hukumar ta ce hadrin motar ya faru ne bayan wata mota ƙirar Peugeot ta ƙwace wa direbanta da misalin karfe 10 na safiyar Laraba.

Shugaban hukumar ta kula da haɗura a Bauchi Yusuf Abdullahi ne ya tabatar da faruwar lamarin yana mai cewar sai da ya dauki jimai’an su sa’a guda kafin su isa inda haɗrin ya afku don miƙasu asibi a basu agajin kulawa, a baban asibitin na Bogoro.

ya kuma shawarci direbobi da su ringa kiyaye dokokin kan hanya da dokokin tuƙi, a duk lokacin da suka hau abin hawa.

Leave a Reply