Mutum daya ya rasu bayan jirgin kasa ya taka wata mota a Abuja

Rudunar ‘yan sandan Abuja ta tabbatar da afkuwar wani hatsari da ya faru a Chikasoro a yankin Kubuwa, da jirgin kasa ya yi taho mu gama da wata mota.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Abuja ta futar, mai magana da yawunta DSP Josephine Adeh ta ce likitocin da ke inda hadarin ya faru sun tabbatar da mutuwar mutum daya.

Ta ce ita ma reshen hukumar jirigin kasa da layin dogon ke karkashin ikonta, sun ƙaddamar da bincike kan faruwar lamarin.

Sannan ta ce za a mayar da alamun kan hanya da gyara wadanda ake da su don kaucewa faruwar makamancin irin wannan hadarin.

Leave a Reply