Mutum biyu sun tsere a Kaduna bayan sun kamu da korona

 

jami’an tsaro na bin sawun wasu mutum biyu da suka kamu da cutar korona a Jihar Kaduna bayan an neme su an rasa tare da kashe wayoyinsu.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an yi wa mutanen biyu gwajin cutar yayin da suke killace a gidajensu amma da sakamako ya fito cewa suna dauke da cutar sai aka neme su aka rasa kuma suka daina daga wayar hukumomi.

Kwamishinar Lafiya ta Jihar Amina Mohammed-Baloni ta ce “abu ne mai hadari” mutanen da suka kamu da cutar su rika kashe wayoyinsu sannan ta ce wajibi ne su rika kai kansu ga hukuma.

Sanarwar da gwamnati ta fitar ranar Lahadi ta ce tuni aka mika wa jami’an tsaro bayanan mutanen sannan ta shawarci mazauna jihar da su kai rahoto ga hukumomi da zarar sun samu labarin inda mutanen suke.