Mutum 160 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo
Hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo sun ce suna ganin akwai kusan mutum ɗari da sittin da suka rasu sakamakon ambaliyar ruwa a Kinshasa babban birnin ƙasar a farkon makon nan.
Gwamnatin ta Congo ta ce mutum ɗari da ashirin ne suka rasu sakamakon ruwa mai ƙarfi da aka yi a ranar Talata. Sai dai tun bayan nan gwamnatin ba ta sake bayar da wasu alƙaluman ba.
A halin yanzu dai an kammala zaman makoki na kwanaki uku da gwamnatin ta ce a yi.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kusan gidaje ɗari uku ruwa ya lalata kuma da dama daga cikinsu an gina su ne a hanyar ruwa