Mutanen da ke bai wa ‘ya’yansu da ke jin yunwa kwaya don su yi barci

Mutanen Afghanistan na bai wa ‘ya’yansu magunguna barci don rashin abinci – wasu sun sayar da ‘ya’yansu mata da sassan jikinsu domin samun kudin abinci. A cikin hunturu na biyu, bayan da ‘yan Taliban suka kwace mulki, aka dakatar da kudaden kasashen waje suke bai wa kasar, rayuwa ta fara wahala.

Abdul Wahab ya ce “’Ya’yanmu na ta kuka, kuma ba sa barci. Ba mu da abinci.”

“Don haka muke zuwa wuraren sayar da magunguna, mu sayi magani mu ba su don su ji jiri.”

Yana zaune ne a wajen Herat, birni na uku mafi girma a kasar, birni ne cike da masu gudun hijira da wadanda suka rasa muhallansu sanadin yaki inda suka zama a gidajen da aka yi da laka.

Abdul na daya daga cikin mutane da dama da suka ka taru a gabanmu. Sai muka tambaye su, shin mutane yawa ne ke ba wa ‘ya’yansu magunguna don su yi barci?

Suka ce “dukkanmu.”

Ghulam Hazrat ya sa hannu a cikin aljihunsa ya fito da magani. Sunan maganin ‘alprazolam’ – maganin da ake bai wa mutanen da ke cikin damuwa.

Ghulam na da ‘ya’ya shida, ɗan auta daga cikinsu yana da shekara daya. Ya ce “har shi ma ina ba maganin.”

Sauran mutanen sun fito da kwalayen kwayoyin escitalopram da sertraline da suka ce suna bai wa ‘ya’yansu. Ana yawan ba wa masu larurar damuwa wadannan magungunan.

Likitoci sun ce bai wa yara wadanda ba su samun isasshen abinci mai gina jiki wadannan magungunan na iya lalata hantarsu, tare da wasu matsaloli kamar gajiya a kowane lokaci da kuma yawan barci da birkita halinsu.

Mun gano cewa za ka iya sayen kwayar magungun biyar a kan kudin Afghanis 10 (naira 150 kenan) a wani kemis da ke birnin, kwatankwacin kudin ledar burodi daya.

Akasarin iyalai suna raba burodi daya a tsakaninsu a kullum. Wata mata ta fada mana cewa suna cin busassshen burodi da safe, da daddare kuma su tsoma shi cikin ruwa don ya yi laushi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce bala’in jin kai na faruwa a Afghanistan.

Yawancin mazan da ke zama a wajen Herat na aikin leburanci ne. Sun kwashe shekaru da dama cikin wahala.

Amma lokacin da Taliban ta karba mulki a watan Agustan bara, ba tare da amincewar kasashen duniya ba, an daina bai wa kasar tallafin kudade daga kasashen waje, lamarin da ya kawo tabarbarewar tattalin arziki da ya yi sanadin rashin aiki ga wasu mazan.

Duk ranar da suka samun aikin yi, suna samun kimanin kudin Afghanis 100 ko kuma sama da dala daya.

Leave a Reply