Mutane Uku ne Suka Rasa Rayukan Su a Wani Rushewar Gini Mai Hawa Hudu a Abuja

Rundunar ƴan sanda a Abuja, babban birnin Najeriya ta tabbatar da rushewar wani gini da rahotanni suka ce mai hawa huɗu ne a yankin Garki.

Sanarwar da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta fitar ta ce ginin ya rushe ne ranar Litinin da daddare.

Ta ce bayan samun kiran waya kan lamarin, kwamishinan ƴan sandan Abuja, Benneth Igweh ya tura jami’ansa zuwa wurin.

A cewar sanarwar, an kuɓutar da mutum uku daga cikin ginin da ya rushe inda kuma aka garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.

Sanarwar ta bayyana cewa rundunar ta ankarar da hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa domin su ɗauki ragamar zaƙulo mutanen da ƙasa ta binne.

Leave a Reply