Ba a bar ƴan Najeriya a baya ba wajen tattaunawa kan fim mai dogon zango da ya shahara a duniya a baya-bayan nan wanda kamfanin Netflix ya samar wato Squid Game.
Mutane sun karaɗe shafukan sada zumunta da muahwara na ƙasar da batun fim ɗin, kamar dai yadda takwarorinsu a ƙasashen duniya ma ke yi.
A shafin Facebook a Najeriya bayanai sun nuna an yi maganar fim ɗin sau kusan da 150,000 a ƴan kwanakin nan.
A shafin Instagram kuma bayanan sun nuna a fadin dunyiya an yi amfanid a maudu’in #squidgame sau 732,183.
Duk an san da fitowar fim ɗin, amma a yanzu ya tabbata a hukumance: Squid Game ya zami shi ne gagrumin fim mai dogon zango da kamfanin Netflix ya taɓa ƙaddamarwa.
An kalli diramar ta ƙasar Koriya sau miliyan 111 a kwanaki 28 na farko inda ya doke shirin Bridgerton da a yake kan gaba da miliyan 82.
An lissafa yawan waɗanda suka kalli fim ɗin ne ga duk wanda ya kalli minti biyun farko.