Musulmin Duniya na bikin Mauludin Annabi (SAW)
Ranar 12 ga watan rabi’ul Auwal rana ce mai matukar girma da daraja ga al’ummar musulmi na duniya, rana ce aka haifi fiyayyan halitta annabi Muhammad SAW.
Al’ummar musulmi a fadin duniya kan yi bikin murnar zagayowar wannan rana da aka haifi fiyayyan halitta Annabi SAW, inda makarantun islamiyu kan gudanar da bukukuwan maulidi a sassa daban daban na duniya.