Musk zai sauka daga shugabancin kamfanin Twitter

Musk zai sauka daga shugabancin kamfanin Twitter

Mamallakin kamfanin Twitter, Elon Musk ya ce zai yi murabus a matsayin babban jami’in kamfanin da zarar ya samu wani da zai maye gurbinsa.

Ya wallafa a shafinsa cewa idan hakan ta faru, shi kuma zai mayar da hankali ne wajen tafiyar da rukunin ma’aikatan da ke kula da rumbun adana bayanai da manhajojin kamfanin.

Matakin na baya-bayan nan da Musk ya ɗauka na zuwa ne kwanaki uku bayan da galibin mutane suka bayyana ra’ayin ya sauka daga shugabancin kamfanin a wata ƙuri’ar jin ra’ayi da ya buɗe.

Sama da mutum miliyan 17 ne suka bayyana ra’ayinsu kuma tun farko Mista Musk ya ce zai mutunta sakamakon.

Leave a Reply