Muric ta bukaci Bankin Polaris Ya nemi Afuwar Musulmin Nijeriya

Kungiyar kare hakkin musulmi ta MURIC ta bukaci mahukuntan bankin Polaris da su nemi afuwar musulmi  ba tare da bata lokaci ba, nan da kwanaki bakwai, ko kuma abukan huldar bankin musulmi su fara kauracewa banki.

Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa da darakta kungiyar farfesa Ishaq Akintola ya fitar aka raba ga manema labarai mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Oktoban 2022

Wannan na zuwa ne sakamakon wani umarni dababban jami’in bankin ya yi ga ma’aikatan sa musulmi da kada su halarci taron sallar juma’a.

Sanarwa tace wata babbar Jami’a abankin na Polaris Damilola Adebara ta aikewa ma’aikatan bankin ta adreshin Email a ranar 11 ga watan 2022 da misalin 12:10 na yamma dake bada umarnin da kada su halarci taron juma’a gami da yin barazanar daukar mataki kan wanda yayi kuskuren ketare wannan doka.

Muric na Alla-wadai da kakkausar murya da wannan kudirin na kiristantar da bankin da kuma kawar da musulmin dake aiki a karkashin bankin na Polaris. wannan ke nuna rashin da’a da kuma rashin kwarewar aiki.

Daga bisani sanarwa ta gargadi bankin cewa wahaniyar sa ta kiyayi ramar musulmi, tare da umartar mahukunta dasu fito fili su nemi afuwar musulmin Nijeriya ko kuma su fara kauracewa bankin.

Leave a Reply