Munguno, ya ce an samu rikice-rikicen siyasa 52 a Najeriya.

Mai bawa shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Babagana Munguno, ya ce an samu rikice-rikicen da ke da nasaba da siyasa akalla sau 52 a jihohi 22 a wata guda.

Munguno, ya bayyana hakan ne a yayin taron bibiyar al’amuan  tsaro da suka shafi ayyukan hukumar INEC a Abuja, inda ya ce  wannan al’amari na ci-musu-tuwo a kwarya dake bukatar daukin gaggawa daga dukkanin masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply