Muna jiran umarnin jam’iyya ta ƙasa kan nasarar Mohammed Abacha – Shekarau

Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar adawa ta PDP a jihar, Ibrahim Shekarau, ya ce suna jiran umarnin da uwar jam’iyyarsu ta ƙasa za ta bayar bayan kotu ta bai wa Mohammed Abacha takarar gwamnan Kanon.

Shekarau ya faɗa wa BBC Hausa cewa “burinmu shi ne ‘yan jam’iyya su natsu, ɓangaren da ya yi nasara da wanda bai yi ba su kwantar da hankalinsu har sai an samu umarni daga jam’iyya”.

A ranar Alhamis ne Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta tabbatar da Mohammed Abacha a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamna a PDP tare da soke zaɓen fitar da gwanin da ya bai wa Sadiq Aminu Wali nasara.

Hakan na nufin ɓangaren shugabancin Shehu Wada Sagagi ne ya yi nasara, wanda ya shirya zaɓen, saɓanin ɓangaren Sanata Bello Hayatu Gwarzo da ke mara wa Sadik Wali baya.

Shekarau ya shiga PDP a watan Disamba bayan rashin jituwa tsakaninsa da jagora kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso.

Leave a Reply