Mun Kwace Miyagun Kwayoyi Na N420bn A Wata 21 – NDLEA

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce ta kama miyagun kwayoyin da kimarsu ta kai ta kusan Naira biliyan 420 tsakanin watan Janairun 2021 zuwa Satumban da ya gabata.

Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ne ya tabbatar da hakan yayin wata zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) a Abuja.

Femi Babafemi Ya ce hukumar ta kuma sami nasarar cafke mutum 19,341 da ake zargi da ta’ammali da miyagun kwayoyin, ciki har da manyan dilolinsu kimanin su 28, inda kuma ya ce kwanan nan za su hada alkaluman watan Satumban da ya wuce.

Kakakin hukumar ya ce lokaci ya wuce da dilolin kwaya za su rika buya suna fakewa da sunan wasu, sannan ya ce hukumar za ta ci gaba da tona asirinsu matukar suka ki su tuba. (NAN)

Leave a Reply