Mun gano maƙiya da ke son ta da hargitsi a Kano, za mu bi su har gida mu zaƙulo

Rundunar ‘yan sandan Kano ta ce jami’an tsaro sun gano wasu mutane da ke shirin tayar da hargitsi a jihar tare da kai hari wasu muhimman wurare ciki har da Majalisar Dokokin jihar.
Kwamishinan ‘yan sanda jihar Muhammad Hussaini Gumel ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai bayan wata ganawa kan al’amuran tsaro a Gidan Gwamnatin Kano ranar Lahadi da daddare.
Ya ƙara da cewa duk inda mutanen suka shiga tabbas za a nemo su a kuma hukunta su.
Ya kuma bayyana cewa duk wanda yake so ya yi amfani da saɓanin da aka samu tsakanin masarauta da gwamnati, domin tayar-da-zaune-tsaye to ba za a ƙyale shi ba da wanda ya tsaya masa a gurfanar da su gaban shari’a.

Leave a Reply