Mun fitar da rai da batun zaɓe saboda ƴan bindiga ke iko da mu

Sa’o’i 48 ‘yan Najeriya su fita domin kaɗa kuri’a a babban zaɓen shugaban kasa da na ‘yan majalisa, al’umma da ke zaune a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro na nuna matsanancin damuwa.

Waɗannan mutane sun kasance a garuruwa da dama da matsalar tsaro ke addaba a yankin arewa maso yammacin kasar, kuma suna ci gaba da kasancewa cikin mawuyacin hali.

Galibinsu a yanzu sun fara fitar da rai daga batun kaɗa kuri’a a zaɓen da ke tafe.

Al’amarin ya yi kamari a wasu kauyuka na yankin karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, inda jama’ar wuraren ke cewa yanzu suna karkashin ikon ‘yan bindiga ne.

A jihar Zamfara kuwa mutanen garuruwa fiye da ashirin suna can suna zaman gudun hijira a garin Bukkuyum.

Girman matsalar

Matsalar tsaron dai na ci gaba da zama babban alakakai a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya.

Yanzu haka akwai mutanen kauyuka fiye da goma na yankin karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, da ba ta batun zabe suke yi ba, a cewar wani mutumin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa.

Ya shaidawa BBC cewa ‘yan ta’adda ke iko da su, ba su da ‘yancin motsawa ku gudanar da wani abu kai-tsaye.

Ya ce suna da katunan zaɓe amma ba su isa su fita ko su je suyi komai ba.

“Ƙauyuka irinsu Ɓaure da ‘Yar Kuka da wasu kusan takwas duk na karkashin ikon ‘yan bindiga da ke mulki da su.

“Don haka babu wani batun zaɓe, domin ‘yan ta’adda ke mulkarmu kuma suna ganin kamar gwamnati ta manta da mu.”

Me hukumomi Katsina ke cewa?

Yayin da muka tuntubi Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina, mai ba gwamnan jihar Katsina shawara kan harkokin tsaro, ya ce ba a manta da mutanen wadannan kauyuka na yankin karamar hukumar Kankara ba.

Ya ce gwamnati na kara basu hakuri, kuma za ta tabbatar da cewa suma sun yi wannan zaɓe.

‘An tilasta mana hijira a Zamfara’

Zamfara

A wasu sassa na yankin karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara yanzu haka ‘yan bindiga sun tilasta wa daruruwan mutanen kauyuka akalla ashirin yin gudun hijira zuwa garin Bukkuyum, kamar yadda wani mutumin yankin ya shaidawa BBC.

Mutumin da muka sakaya sunansa ya ce an tarwatsa yankunansu, kuma hukuma ta fita daga batun su, ba sa jin komai kan batun zabe.

“A takaice bamu da komai sama da rayuwarmu.”

Ita ma Wata mata, cikin ‘yan gudun hijirar ta bayyana yadda suka tsere daga kauyukan nasu tana mai cewa:

“Ai bamu da wani ‘yanci ko wajen kwana da abinci bamu da shi, kullum muna cikin sauya matsuguni.

“Rayuwar mu na cikin ƙangi domin ba mu da wani sukunni komai ya yi mana tsanani.”

Me hukumomin Zamfarar ke cewa?

BBC ta yi kokarin kiran wayar Kwamishinan tsaro na jihar ta Zamfara DIG Mamman Tsafe mai ritaya, amma ba mu same shi ba.

Kuma har ya zuwa lokacin wallafa wannan labari ba mu sami amsar sakon da muka aika masa a rubuce ta waya ba.

Sai dai bayanai sun nuna cewa, akwai garuruwa da dama da ke cikin irin wannan tarkoko a shiyyar ta arewa maso yammacin Najeriya.

Leave a Reply