Mozambique za ta fara amfani da ‘yan kato da gora kan masu ikirarin jihadi

Majalisar Mozambique ta amince da kudurin amfani da ‘yan kato da gora a yakin da take da masu ikirarin jihadi a arewacin lardin Cabo Delgado.

‘Yan kato da gora suna taimakon sojoji da kawayensu daga Rwanda da kuma yankin kudancin Afrika a yakin da suke da masu jihadi a lardin.

Ministan tsaro Cristovao Chume, wanda ya gabatar da wannan kuduri gaban majalisar, ya bayyana cewa sojojin Muzambique ba su da karfin da za su yaki wadan nan mutane da ake fama da su, su kudai.

Ya ce akwai bukatar gaggawa ta fara amfani da ‘yan bindiga domin karfafa sojoji, da kuma kokarin karkade sauran mayakan.

Yace za su rika kare unguwanni da kuma dukiyoyin al’umma, irin dai hanyoyin da aka yi amfani da su a wasu yankunan a baya.

Leave a Reply