Ministan shari’a ya goyi bayan kudurin karin albashi ga alkalan kasar nan

Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi mai mukamin SAN, da Babban alkalin alkalan Najeriya, Mai shari’a Olukayode Ariwoola, da kungiyar lauyoyin Najeriya sun goyi bayan kudurin karin albashi ga alkalan kasar nan.
Bangarorin sun ba da wannan goyon baya ne a wani taron jin ra’ayin jama’a kan Kudirin dokar da za ta tsara albashi da alawus alawus ga ma’aikatan shari’a a Najeriya bisa dokar 2024, wanda kwamitin majalisar dattawa kan harkokin shari’a ya gabatar.
A cewar AGF, a cikin rahoton kwamitin, tsakanin watan Mayu 1999 zuwa Maris 2011, Gwamnatin Tarayya ta duba albashi da alawus alawus na ma’aikatan gwamnati da masu rike da mukaman siyasa, musamman a shekarar 2000, 2005, 2007 da kuma 2011.
Ya kuma ce, an kuma kafa sabbin tsare tsare na mafi karancin albashi na kasa a cikin wannan lokaci, duk da cewa an sake duba albashin jami’an shari’a sau biyu a lokaci guda.

Leave a Reply