Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce idan ba a kara kudin wutar lantarki nan da wata uku ba, za a rasa ta a Najeriya.

Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce idan ba a kara kudin wutar lantarki nan da wata uku ba, za a rasa ta a Najeriya

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da yake amsa tambayoyi a gaban kwamitin majalisar dattawa da ke bincike kan karin kudin wutar da hukumar kula wutar lantarki ta yi.

Kwamitin Majalisar Dattawa kan wutar lantarki ƙarƙashin jagorancin Sanata Enyinnaya Abaribe ya ki amincewa da karin farashin wutar.

Ya bayyana cewa, “Gwamnati na buƙatar kashe Dala biliyan 10 a kowace shekara har tsawon shekaru 10 idan ana son a gyara masamar wutar lantarki.

Ya kuma ce gwamnati ba ta da niyyar bayar da tallafi a harkar lantarki, wanda hakan ne ya tilasta wa ɓangaren neman hanyar yin mai yiwuwa domin tabbatar da cewa Najeriya ba ta tsunduma cikin duhu ba.

Leave a Reply