Ministan kwadago da nagartar aiki A Najeriya Chris Ngige yace yajin aikin gargadi na makwanni 4 da kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ta tsunduma tamkar sun dauki hutu ne kawai kasancewar kungiyar malaman bata sanar da ofishinsa aniyarta ba kafin ta tsunduma yajin aikin.
Ngige ya kuma bayyana cewa kungiyar malaman jami’o’in tayi biris kuma bata yi biyayya ga yarjejeniyar da aka cimma ba da majalisar kungiyar addinai ta kasa wadda ke karkashin Me alfarma sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa’ad da shugaban kungiyar kiristoci na kasa Rabaran Samson Ayokunle na cewa kungiyar ba zata sake tafiya yajin aiki ba har sai ta tuntube su.
Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar malaman jami’o’in ta kasa ta tsunduma yajin aikin gargadin nata ne a ranar 14 ga watan fabrairun nan da muke ciki biyo bayan kammala taron majalisar zartarwar ta wanda ya gudana a jami’ar jihar Lagos.
Kungiyar dai ta zargi gwamnatin tarayya da cigaba da yin biris tare da karya alkawari da yarjejeniyar da suka cimma da ita wadanda suke da jibi da hakkokin ‘ya’yanta da tsarin biyanta albashi.